By Abbas Yakubu Yaura
Ga masu aikin sa kai na N-Power Batch C wadanda matsayinsu na biyan albashin su kwanan nan ya canza daga “rashin biya” zuwa “na jiran tsammani”, yakamata su lura da matakan dake ƙasa wanda shine hanyoyin da za a bi kafin biyan kuɗi.
Na farko Idan kai dan agaji ne na N-Power Batch C kuma matsayinka na biyan albashi ya nuna jiran tsammani wato ‘PENDING’ kawai yana nufin ana sanya ka cikin tsarin biyan albashi, da zarar ka shiga lissafin wadanda za’a biyasu albashin yana nufin damar biyan ku ya kai kashi 100% .
Na biyu Daga jiran tsammani wato “PENDING” matsayin albashin ku zai canza zuwa matakin jira “PROCESSING” wannan mataki kawai yana nufin an aiko muku da kuɗinku da alawus ɗin ku zuwa bankinku daga Babban Bankin Najeriya, kuma damar samun kuɗin ku a wannan matakin shine kashi 100% na biyan kudin.
Na uku Da zarar halin biyan kuɗin ku ya nuna an biya wato “PAID” yana nufin an ƙididdige asusun ku, idan halin biyan kuɗin ku ya nuna an biya ku, yana nufin damar ku na biyan kuɗi ne wato shima kashi 100%, a wannan matakin ana shawartar duk masu aikin sa kai na N-Power Batch C, dasu ci gaba da bincika mamhajar su na banki ko amfani da bankin su na USSD don bincika idan an sami ƙaruwar biyan kudin dake cikin ma’auni na asusun ku.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa da yawa daga cikin masu aikin na sakai wasu daga cikin su har yanzu basu sami albashin su ba tun bayan da ma’aikatar jinkai da kula da bala’oi da cigaban al’umma ta fara biyan albashin aranara 11 ga watan Nuwamba.