Hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar turai wato Uefa ta bayyana ranar da zata raba rukunin jaddawalin gasar zakarun ƙwallon ƙafa ta nahiyar turai wato sabuwar kakar wasa daza’a shiga ta shekarar 2020 zuwa 2021, sai dai ana ganin cewar gasar ta bana zata iya zuwa da sabon salo ganin yadda kusan kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta yi gyara wajen sayen ‘yan wasa.
Sai dai akwai wani abu da masana harkar wasanni suke cewa da wahala kaga ƙungiyar ƙwallon ƙafan da bata da wannan gasa a shekarun baya aga ta lashe gasar, I da mafi yawa duk ƙungiyar ƙwallon ƙafan datake dashi to itace take sake lashe gasar wanda abin ya zama kamar gado a yadda alƙaluma suka nuna.
Ga babban misali a shekarun baya an fafata wasannin ƙarshe tsakanin wadda ta saba lashe kofin da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da basu taɓa lashe wannan gasa ta zakarun turai ba amma kuma da wahala kaga wadda bata da shi ta lashe gasar, idan za a iya tunawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid dake ƙasar Andalus ta fafata wasannin ƙarshe guda biyu da abokiyar hamayyarta ta cikin gida wato Athletico Madrid amma duk wasannin ƙarshen guda biyu Real Madrid ce mai lashe wa.
Haka zalika a wannan kakar wasan da ta gabata an fafata wasannin ƙarshe tsakanin zakarun gasar wato Bayern Munich da Paris Saint Germain idan Bayern Munich ta zamo zakara bayan ta jefa ƙwallo 1 tilo a ragar ƙungiyar Paris Saint Germain, idan za a iya tunawa ita PSG batazo wasan ƙarshe ko sau ɗaya ba tunda aka kafa ƙungiyar, haka zalika idan ba a manta ba a wasan ƙarshe shugaban na PSG wato Nasser Al-Khilafi ya bayyana cewar matuƙar PSG ta zamo zakara to akwai wasu manyan kuɗaɗe na garaɓasa daza a baiwa kowanne ɗan wasa amma kuma suka gaza lashe gasar.
Wannan gasa ta zakarun nahiyar turai dai wadda tafi lashe gasar itace Real Madrid kuma hasali ma itace ƙungiyar ƙwallon ƙafan da ta assasa wannan gasa tun a shekarar 1955 inda kuma a shekarar 1956 ta fara lashe gasar inda sai da ta jera ahekaru 5 a jere tana zamowa zakara, a yanzu dai jimilla tana da kofin guda 13 a tarihi, haka idan za a iya tunawa a shekarar 1990 aka sauyawa gasar suna amma tun lokacin babu wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa data lashe sau biyu a jere amma ita Real Madrid ta yi haka a ƙarƙashin jagorancin mai horas wa Zinedine Yazid Zidane.
Hukumar ta Uefa ta sanya ranar 1 ga watan gobe na Oktoba domin raba jaddawalin rukunin gasar zakarun ƙwallon ƙafan ta nahiyar turai inda a waccan ranar ce kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa zata san da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan daza ta fafata a rukuni a sabuwar kakar wasa mai kamawa ta 2020 zuwa 2021.
Danagane da yadda za a raba jaddawalin rukunin gasar jaridar www.dimokuradiyya.com.ng ta tattauna da Hajiya Hajara Umar dake unguwar Badarawa a jahar Kaduna wadda ita mai goyon bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ce, inda jaridar ta tambayeta cewar Manchester United zata fafata gasar zakarun turai a sabuwar kakar wasa daza a fara, sannan gashi a kakar wasan data gabata Manchester bata halacci gasar ba shin ko yaya take ganin Manchester a kakar wasa ta bana musamman a gasar zakarun turai?
“To Manchester United dai har yanzu muna da matsaloli sosai ganin cewar Hausawa na cewa kayi cefane mai kyau kasha miya mai zaƙi, wato Manchester United ta zama kamar mutum ne yana ciwon ƙafa amma sai aje a sayo maganin ciwon ciki a bashi, saboda matsalarmu itace ‘yan wasan baya, amma anje an sayomana wani Van de Beek bayan muna da isassun ‘yan wasan tsakiya, matsalarmu itace ‘yan wasan baya da kuma lamba tara mai wayo da gwaninta wajen jefa ƙwallo a zare. Wani babban abin haushi ma shine a wasan da muka fafata na farko na gasar Firimiya har gidanmu Crystal Palace ta lashe mu da ƙwallaye uku, kaga ta yaya zamuce zamu buga gasar Champions League a haka, kawai amsar itace har yanzu akwai matsala a wajen mahukuntan ƙungiyar mu ta Manchester United”
An bayyana cewar dai a wannan rukuni da hukumar zata raba tuni a tukunyar farko akwai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool da dai sauran manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daga ƙasashe daban-daban na nahiyar ta turai inda ranar kawai ake jira tazo domin fitar da jaddawalin kamar yadda aka ambata.