Yadda zan haɗa kan Najeriya idan aka zabe ni – Peter Obi
Dan Takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi ya yi nuni da yadda gwamnatinsa za ta hada kan Najeriya idan aka zabe shi a 2023.
Obi ya ce gwamnatinsa za ta yi kokarin sake hade Najeriya ta hanyar amfani da tanade-tanaden doka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da alamu muna cikin ruɗani a Najeriya – Bola Tinubu
Da yake magana yayin wani taro a birnin Charlotte na jihar North Carolina a ranar Laraba, Obi ya ce sake duba kundin tsarin mulkin Najeriya zai kasance wani bangare na sake fasalin bukatun ‘yan Najeriya baki daya.
Ya ce: “Za mu nemi sake hade Najeriya ta hanyar bin ka’idojin tsarin mulki na daidaiton wakilci a hukumomin tarayya da kuma farfado da tunanin zama na kowani ‘yan kasa ta hanyar hada kai da isassun wakilcin mata, matasa da nakasassu a gwamnati.”
Obi ya ce sake duba kundin tsarin mulkin zai kunshi ayyukan majalisa, zartaswa, da na shari’a, yana mai kara da cewa “Daga karshe al’ummar Najeriya za su yanke shawara”.
Ya kuma yi nuni da cewa, gwamnatinsa za ta sake tabbatar da rawar da Najeriya ke takawa a harkokin Afirka ta hanyar yin aiki mai ma’ana, ta hanyar amfani da tarukan da ake da su na yankuna da na shiyya-shiyya da kuma dandalin tattaunawa kan kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu da kuma masu tasowa.
A wani labarin kuma: Jam’iyyar APC a jihar Taraba za ta sasanta Fusatattun Ƴan jam’iyyar
Jam’iyyar APC reshen Jihar Taraba, ta fara wani yunƙuri na sasanta dukkanin Fusatattun ƴaƴan Jam’iyyar da ke cikin Jihar.
A ranar Alhamis ɗin data gabata ne mambobin Jam’iyyar suka shiga tattaunawa da shugabannin jam’iyyar a Jalingo babban birnin jihar.