Yajin aiki: A bayyane yake FG, ASUU babu abin da za su yi asara — Ƙungiyar Ɗalibai
Majalisar Shugabannin Ƙungiyar Ɗalibai (CSUP) ta koka kan yadda ta ke rasa Dalibai sakamakon kashe-kashen da ƴan bindiga suke yi musu sakamakon tsawaita zamansu a gida a dalilin yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU.
KARANTA WANNAN LABARIN:Akwai Cin Hanci Da Rashawa A Karkashin Gwamnatin Buhari Fiye Da PDP – Tsohon Jigon APC, Bwala
Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai (SUG) na Jami’ar Fasaha ta Tarayya (FUT) Minna, Mista Ishaka Yahaya, ya yi magana a madadin dukkan shugabannin SUG na manyan Makarantun Najeriya a wani taron Manema Labarai a Abuja ranar Alhamis.
Yahaya ya ce babu abin da Gwamnatin Tarayya da Kungiyar ASUU suka yi asara a cikin yajin aikin, inda ya ce dalibai da dama da za su je makaranta amma sun koma yin wasu ayyuka, amma ana yin garkuwa da su ana kashe su.
Ya Buƙaci Gwamnati da ta duba buƙatun ASUU ta kuma kula da su domin su koma makaranta.
“Gaskiya ne idan suka ce, lokacin da giwaye biyu suka hadu, ciyawa ce kawai ke shan wahala.
“A bayyane yake a nan Gwamnatin Tarayya da kuma ASUU ba su da wani abin a zo a gani a wannan fada.
“Wannan ya faru ne saboda a yayin da ake ci gaba da yajin aikin, albashin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya na ci gaba da tafiya, kuma a ƙarshen yajin aikin, babu abin da zai hana albashin ƴan kungiyar ASUU ma ya shiga asusun su.
“Wanda kawai abin takaici ne cewa daliban Najeriya kaɗai zasu yi asara wadanda suka rasa komai.
“Ko da an janye yajin aikin, da yawa daga cikin ɗaliban ba za su iya yi wa ƙasa hidima ba saboda yawaitar shekaru.
“Da yawa dalibai bayan kammala karatun ba za su iya samun ayyukan Gwamnati ba saboda la’akari da iyakokin shekarun,” in ji shi.
Yahaya ya lura cewa yajin aikin ya kara yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi, karuwanci da ‘yan daba, da dai sauran wahalhalu da rashin manufa ta daliban Najeriya wadanda a karkashin yanayi na yau da kullun, ya kamata su kasance a makaranta don samun ilimi.
Ya ce daliban Najeriya da cibiyoyin karatu sun fuskanci rashin tsaro, don haka a kullum dalibai sun zama wadanda ‘yan bindiga ke garkuwa da su a kullum.
“Don haka muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta biya bukatun ASUU cikin kankanin lokaci domin rashin yin hakan ba zai bar mu da wani zabin da ya wuce mu ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana ko da a cikin wannan rashin tsaro.
“Domin yana da kyau a mutu don wani abu da a rayu ba komai,” in ji shi.