Babban Mai rikon Mukamin Sufetan Yan Sandar Najeriya Usman Baba ya gargadi yan sanda a Jihar Kaduna da kada su bari ana kukan targade kuma a samo karaya.
Sufetan yana wannan magana daidai lokacin da ma’aikata a Jihar ta Kaduna ke rana ta farko a yajin aikin da suka Tsunduma da kuma zanga-zanga.
Usman Baba cikin wata sanarwa da ya fitar bayan wannam mataki, ya ce ba za a yi kasa a gwiwa ba wajem kara jibge jami’an tsaro a jihar don kare rayukan jama’a.
Ya ce yanzu hala ana ta shirye-shiryen sake jibge jami’an tsaron yan sandar jingim musamman a manyan hanyoyi don kare aukuwar wata tarzoma.