Yayin da Kungiyar Kwadago ta kasa ke tsunduma yajin aiki a yau Litinin a Jihr Kaduna, Gwamnan Jihar Mallam Nasir el-Rufa’i ya bugi kirjin cewa su yi duk abinda za su yi yana daidai da su, har ma da kanwa uwar gami wato Jam’iyyar PDP a cewar shi.
Da ma tun a yammacin jiya Lahadi ne Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jihar Kaduna ya katse dukkanin layukan bada wutar lantarkin, lamarin da ya jefa Al’ummar jihar cikin matsanancin duhu da tashin hankali.
Matakin na Kamfanin kuma ya biyo bayan wani umarni ne da uwar Ƙungiyar kwadago ta bayar cewa ma’aikatan Jihar su tsunduma wani yajin aikin gargadi.
Ko da yake rahotanni sun bayyana cewa wasu ma’aikata a Jihar na dari-darin shiga yajin aikin, ganin cewa gwamnatin Jihar ta sha alwashin daukar sunayen wadanda suka je aiki a yau.
A ranar Asabar ne dai gwamna el-Rufa’i ya bugi kirjin cewa ba zai bar gwamnatinsa kawai kara zube ba, yana mau cewa gwamnatin tasa ba za ta iya rika cire kaso 84 zuwa 96 na tallafin ta daga gwamnatin tarayya ta banzatar da shi a albashi ba.
A Jiya Lahadi ne dai Shugaban Ƙungiyar NLC ta kasa Kwamared Ayuba Wabba da wasu jiga-jigan kungiyar suka hallara a Kaduna don wata ganawar sirri.
Kazalika da yake maida martani ga sakon PDP na Tuwita kan yajin aikin NLC din, el-Rufa’i ya ce a shirye yake da dum wani dan kanzagi mai shirin tada zaune tsaye.