Kungiyar Malaman Kwalejojin Kimiya da Fasaha ASUP ta yi barazanar tsunduma yajin aikin na har sai baba ta gani tare da janye ayyukan mambobin ta a fadin kasar nan.
Yajin aikin dai kamar yadda kungiyar ta sanar za a fara shi ne a ranar talata shida ga watan Afirelun shekarar da mu ke ciki.
Shugaban Kungiyar ta Kasa Mista Anderson Ezeibe wanda shine ya ayyana wannan mataki na kungiyar yayin zantawa da manema labarai a Katsina, ya ce dole ne kungiyar ta tsunduma wannan yajin aiki muddin gwamnatin ba ta biya matya bukatun ta ba.
A cewar shugaban Kungiyar, akwai bukatu da dama da kungiyar ke da su a gurin gwamnati wadanda aka gaza biya mata su, don haka ne ya sa ta ga babu wata hanya ta nuna wa gwamnati fushin ta face fadawa yajin aikin.
Don haka ne kungiyar ke kara jaddada wa mambobin ta cewa su yi damarar shiga yajin aikin wanda kuma ba za su dawo bakin aiki ba har sai an biya musu bukatun su.