Guda cikin dattawan Kasar nan Edward Clerk ya bukaci ministan Ilimin kan ya karbi ragamar tattaunawar da ake da kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU, domin hakan zai taimaka wajen kawo karshen yajin aikin da suke yi.
Edward ya bayyana hakan yayin wata hira ta musamman da kamfanin dillancin labarai na Najeriya yayi da shi, A Abuja, inda ya ce Ministan Ilimin Adamu Adamu zai fi sauran sanin makamar kawo karshen yajin aikin da suke yi.
Ya kara da cewa Ilimi ba abun wasa bane, da ya kamata a baiwa wani can na daban domin kula da shi, wanda a cewar sa kamata yayi ace abar masana bangaren suyi abinda ya kamata, din n kuwa yajin aikin na cutar da Tattalin Arzikin kasa.
Ya kuma ce Banda rushewar tsarin karatu da yajin aikin ya haifar a Najeriya, kazalika yawan aikata laifukan shima ya karu matuka, Banda yan sace sace da ake samu nan da can.
”A Kowace kasa Ilimi shine farko, daga lokacin da ka samu ilimi wadatacce to kuwa wannan al’umma da kake a cikinta zata tsira, sannan kuma tattalin arziki zai bunkasa.”
Yanzu ka duba Akanta Janar na Kasa, an kama shi da laifin sace Naira biliyan 80, wanda kusan rabin kuɗin da ASUU ke bukata ne shi kadai ya wawure,” inji shi.
A dan haka ne yace a zaben 2023, za a samu tsaiko matuka kamar yadda aka samu a baya, matsawar gwamnati bata gaggauta kawo karshen wannan matsala ba.