Malam Usman Abubakar-Rimi, wanda dalibi ne a shekarar karshe a fannin likitanci da tiyata a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto (UDUS), ya koma mai siyar da abinci a kan titi saboda tsawaitar yajin aikin da malaman jami’ar suke yi.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a ranar Juma’ar nan a Sokoto, Abubakar-Rimi ya ce ya dauki wannan matakin ne domin su samu rayuwa mai inganci yayin da yajin aikin ya tilastawa dalibai barin makaranta.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Abubakar-Rimi, wanda ya mallaki wajen siyar da abinci da taliyar yara ta indomi a Unguwar Diplomat a cikin birnin Sokoto ya bayyana cewa yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta shiga ya ba shi cikakkiyar dama.
Ya bayyana cewa ya tsunduma cikin harkar siyar da abinci a cikin watanni biyun da suka gabata inda ya bayyana sana’ar a matsayin mai riba.
Karanta kuma: Gwamnatin Buhari Ta Tallafawa Wata Jihar Da Kayan Abinci
“Na dauki hayar shago, na dauki ma’aikata guda takwas masu sarrafa shayi da hada-hadar taliyar yara, ina sayar da kayan sha na kwalba da gwangwani, masara, shinkafa da wake, miya na pepe da nama tare da kasuwancin Point of Sell wato (POS).
“Ana sayar da farantin abinci daga Naira 200 zuwa sama gwargwadon bukatun abokin ciniki,” in ji Abubakar-Rimi.
Ya bayyana cewa ya mallaki wani shago a kan titin Fodio shima a cikin birnin Sokoto inda yake sayar da kayan sawa na maza da mata, hula, da takalmi.
“Na yi farin cikin ganin cewa na zama ma’aikaci domin a halin yanzu na dauki mutane 10 a cikin shagunana biyu.
Ya kara da cewa, “Na dogara ga shagunan samun kudin shiga masu kyau, saboda ba na tambayar iyayena kudi duk da cewa an rufe makarantu.”
Abubakar-Rimi ya ce bai samu wani lamuni ko shirin karfafa matasa don fara sana’ar ba.
“Duk da haka, na yi amfani da damar kulle-kullen COVID-19, yayin bala’in kuma na fara kasuwancin rarraba kwai da kaji inda na yi hulɗa da gidajen abinci don samun wadatuwa.
Abubakar-Rimi ya kara da cewa sana’o’in na da dimbin alfanu, ya kuma ja hankalin matasa da su rika tunanin hanyoyin dogaro da kai da kuma zage damtse wajen gudanar da ayyuka masu inganci.
“Na tsara wani tsari mai dorewa inda aka bude rajista don mafi girman rikodi, sarkar samar da kayayyaki da sauran hanyoyin gudanarwa,” in ji Abubakar-Rimi.
A wani labarin kuma: Kyandar Biri: Najeriya Ce Tafi Yawan Matattu Da Kamuwa Da Cutar A Afirka–WHO