Karamin Ministan Ilimi, Rt Hon Goodluck Nanah Opiah, ya bayyana dalilan da suka sanya gwamnatin tarayya ta tsaya kan tsarin babu aiki, babu biyan albashi ga malaman jami’o’i ASUU.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kungiyar malaman jami’o’in, ASUU, tuni tayi Allah wadai da wannan tsarin na gwamnatin tarayyar.
KARANTA ANAN: Atiku Ya Gana Da ‘Yan Takarar Gwamnonin Jam’iyyar PDP A Abuja
Ministan, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar ta hannun mai taimaka masa kan kafafen yada labarai, Kelechi Mejuobi, ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta magance rikicin, dake tsakaninta da ASUU.
Opiah, wanda ya kai ziyarar aiki a Jami’ar Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, yayin da yake nadamar yadda yajin aikin ya jawo koma baya a fannin ilimi inda gwamnati, dalibai, iyaye, da malamai suka yi asara, ya bukaci masu ruwa da tsaki da su sanya baki.
Ya kuma yi kira ga shugabannin majalissar gudanarwar jami’o’i da su shigo cikin lamarin su shawo kan ASUU ta sake duba matsayarta.
A wani labarin kuma: EFCC Ta Saki Wani Kakakin Majalisa Bayan Awanni 48 Da Kama Shi
Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta saki kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo bayan shafe sa’o’i 48 a hannun ta.
Oluomo dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Ifo ta 1 a majalisar dokokin jihar Ogun ya koma gidansa dake Ifo a safiyar ranar Asabar din nan.