Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa za ta bi sahun kungiyar kwadago ta Najeriya NLC domin nuna rashin amincewa da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ke yi.
Wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 22 ga watan Yulin shekarar 2022 wanda babban sakataren kungiyar, Joe Ajaero ya fitar, ta bukaci dukkan mambobin kungiyar su shiga cikin zanga-zangar da NLC ta shirya gudanarwa.
Jaridar Dimokiradiyya ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne kungiyar NLC ta sanar da fara zanga-zangar hadin gwiwa da sauran kungiyoyin kwadago domin nuna adawa da yajin aikin da ma’aikatan jami’o’in kasar ke yi tun ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2022.
Takardar ta ci gaba da cewa, “Bisa ga umarnin NLC da kuma matsayinmu wanda aka bayyana a taron kwamitin gudanarwa (CWC) da majalisar zartarwa ta kasa (NEC) na kungiyar mu”.
“An umurci dukkan mambobin kungiyar da su fito fili su shiga cikin zanga-zangar hadin kan NLC da ASUU don nuna rashin amincewarsu da ci gaba da rufe manyan makarantun kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 26 da 27 ga Yulin shekarar 2022.
“Ana karfafa muku gwiwa da ku yi aiki tare da shugabannin Majalisar Zartarwa ta Jiha (SEC) na kungiyar a jihohinku” inji sanarwar.
A wani labarjn kuma na daban.
Bayan Yi Masa Tiyata, A Karshe An Sallami Osibanjo Daga Asibiti
An sallami mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo daga asibiti sakamakon samun nasarar yi masa tiyata da gyaran jiki.
Mataimakin shugaban kasar ya shafe kwanaki 7 a asibitin Duchess na Legas tun ranar 16 ga watan Yuli, inda aka yi masa aurin karaya.
Babban Likita na Mataimakin Shugaban Kasa, Dr Nicholas Audifferen, ya bayyana hakan a ranar Litinin cewa aikin da akayi wa magaimakin shugaban nasa ya yi nasara “ba tare da wata matsala ba.”
“An kwantar da Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, SAN a Asibitin Duchess International Hospital, dake jihar Legas, a ranar Asabar da ta gabata, 16 ga Yulin shekarar 2022, saboda karayar da ya samu. Kuma An yi masa tiyatar gyara ba tare da wata matsala ba.”
“An kwantar da shi tsawon kwanaki 7 a lokacin tiyatar. bayan tiyatar da aka yi masa. An sallame shi kuma yanzu yana samun sauki,” inji shi.
Ya kara da cewa mataimakin shugaban kasar ya mika godiyar sa ga ma’aikatan asibitin bisa irin kulawar da suka yi masa tare da aiki cikin nuna kwarewa da inganci, sannan ya yaba da fatan alherin da shugaban kasa Buhari ke yi da kuma duk wadanda suka aiko masa da sakon fatan alheri.
Ya ce, “Farfesa Osinbajo yana godiya ga daukacin ma’aikatan asibitin karkashin jagorancin babban jami’in gudanarwa, Dokta Tokunbo Shitta-Bey da Daraktan Likitoci, Dokta Adedoyin Dosunmu-Ogunbi bisa kwarewa da ingancin kulawa da suka nuna.
“Mataimakin shugaban kasar ya kuma yaba tare da fatan alherin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ‘yan Najeriya daga kowane bangare na rayuwa da kuma kowa da kowa a gida da waje domin fatan alheri.
“Mataimakin Shugaban kasan zai ci gaba da murmurewa a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.”