Ministan ilimi, Adamu Adamu, tare da masu ruwa da tsaki irin su magatakardar hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sikandire, Farfesa Ishaq Oloyede; Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, Farfesa Abubakar Rasheed; Emeritus Peter Okebukola da Nimi-Briggs; tare da dukkan shugabannin jami’o’in tarayya da masu goyon bayan shugabannin jami’o’in tarayya sun fara wani zama na musamman.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa zaman ya kasance na sirri ne, kuma zai mayar da hankali kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in take yi yanzu haka.
“Zan so in yi tambaya cikin girmamawa cewa shugabannin ‘yan jarida su yi mana uzuri domin mu fara shawarwari,” in ji Adamu Adamu.
KARANTA ANAN: An Kama Likitan MDD Na Bogi A Abuja
Tun da farko dai Ministan ya koka da yadda kungiyar ASUU ta kasa janye yajin aikin da suke yi duk da tsoma bakin da gwamnati ta yi.
ASUU ta shiga yajin aikin ne a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, 2022 biyo bayan abin da kungiyar ta yi wa lakabi da gazawar gwamnati wajen biyan wasu bukatu.
A wani labarin kuma: An Buƙaci APC ta sake duba Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa
Gamayyar masu ruwa da tsaki a shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya na jam’iyyar APC, sun buƙaci kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC (NWC), da ya gaggauta sake duba zaben Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar.
Babban sakataren kungiyar Dauda Yakubu, yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, ya shawarci jam’iyyar da ta gaggauta yin wani abu don magance matsalar da ta kunno kai sakamakon matakin da ta dauka a kan tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi.
Ta ce matakin na haifar da rarrabuwar kawuna, kiyayya da kuma shakku a tsakanin ‘yan Najeriya.