Daga: Abbas Yakubu Yaura
Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ya bayyana cewa an dauki matakin sasantawa na son rai domin ganin an gaggauta warware yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yi.
Ngige ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wajen wani taron karawa juna sani na kwana uku kan matakan ma’aikata da warware takaddamar Najeriya a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kasuwanci: Satar Mai Ita Ce Ta Jawo Faduwar Naira, Tabarbarewar Tattalin Arziki – Shell
Kwamitin sulhu na masana’antu (IAP) tare da hadin gwiwar kungiyar kwadago ta duniya ILO ne suka shirya taron.
Ngige ya ce an dauki matakin sasantawa ne na son rai domin kada a jinkirta aiwatar da shawarwarin da malaman da suke yajin aiki.
Ministan ya ce, “Da zan iya mika lamarin ga Hukumar IAP ko kuma Kotun Masana’antu ta Kasa (NICN).
“Amma na yi amfani da hankalina don auna lamarin don sanin ko zai haifar da jinkiri wajen warware takaddamar a cikin shari’a.”
Ngige, ya tuna cewa ASUU ta shiga yajin aikin ne a ranar 14 ga watan Fabrairu, kuma an fara sasantawa na son rai a ranar 22 ga watan Fabrairu, daga bisani kuma, a ranar 1 ga watan Maris.
Ya ce, “Batutuwan biyu da suka yi fice, su ne ka’idojin hidima, wadanda bisa yarjejeniyar shekarar 2009, za a sake duba su duk bayan shekaru hudu.
“Bita na karshe shine a shekarar 2013 kuma mun fara bitar ne a shekarar 2018 karkashin Wale Babalakin a matsayin shugaban kwamitin sake tattaunawa. Ba mu iya gamawa ba saboda Babalakin ya tafi.
“Sabon kwamitin da Munzali ya jagoranta ya zo. Munzali ya gama aikinsa ya sanya rahotonsa a ma’aikatar ilimi ta tarayya.”
Ngige ya bayyana cewa dukkanin kwamitocin da suka hada da na Onosode na baya, duk kwamitocin cikin gida ne na ma’aikatar ilimi.
Ya ce, “Da zarar kwamitocin sun gama sai a aika da kayayyakinsu.
“Babban batu a nan shi ne albashi da sabun tashi. Anan suke kafin ASUU ta fara yajin aiki.
“Idan wata ƙungiya tana son mu mayar musu da wani al’amari don su sake duba su, ku taimake su. Abin da kuke kira sulhu na son rai ke nan.