Kungiyar dalibai ta kasa NANS ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi a Legas a yau Talata, don nuna takaici da ci gaba da rufe jami’o’in.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda daliban suka ci cincirundo a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a ranar Litinin.
Matakin da daliban suka yi ya jawo wa matafiya da masu ababen hawa fuskantar wahala domin an fuskanci matsalar cunkoson ababen hawa a sassa daban-daban na jihar.
An sake jinkirta tashin jirage da dama yayin da wasu fasinjojin suka yi kewar jiragensu saboda toshewar da daliban suka yi.
KARANTA ANAN: Farashin Gas Ya Karu Sama Da Kaso 100 A Shekarar 1 – NBS
A baya dai daliban sun sha alwashin ci gaba da zanga-zangar yau a Legas har ma da tashar jiragen ruwa domin neman a kawo karshen yajin aikin ASUU na watanni 7.
Sai dai a wata hira ta wayar tarho a ranar Talata, Shugaban NANS na Legas, Kwamared Olusesi Tolulope, ya ce an dakatar da zanga-zangar ne sakamakon tsoma bakin kakakin majalisar wakilai, Mista Femi Gbajabiamila.
Ana sa ran Gbajabiamila zai gana da Ministan Ilimi, Adamu Adamu, da shugabannin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da sauran masu ruwa da tsaki kan yajin aikin.
A wani labarin kuma: Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Biliyan Dubu 40
Jimillar bashin da ake bin Najeriya ya tashi daga Naira tiriliyan 41.60 (dala biliyan 100.07) a watan Maris zuwa Naira tiriliyan 42.84 (dala biliyan 103.31) a watan Yuni.
Ofishin kula da basussuka (DMO) karkashin jagorancin Patience Oniha ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar yau Talata.