Wani daliba ta bukaci wata babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta ba da umarnin dakatar da kudaden da ake baiwa fadar shugaban kasa, ma’aikatu da gwamnoni duk wata har sai an yanke shawarar daukar matakin da malaman jami’o’i suka dauka kan masana’antu.
Soohemba Agatha Aker, wadda daliba ce mai karatun digiri na farko kuma shugaban kungiyar dalibai ta jami’ar jihar Benue (BSU), ta dau matakin ne a madadin daliban da aka tsawaita zamansu a gida saboda yajin aikin Jami’o’i.
A karar da lauyanta Chukwuma Machukwu-Ume (SAN) ya shigar a ranar 21 ga watan Satumba, 2022, Aker ta kuma bukaci a dakatar da biyan albashi da alawus-alawus ga dukkan manyan sakatarorin, da shugabannin ma’aikatun gwamnati da na ministoci, da duk shugabannin Jami’o’in da suke yajin aikin.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ta kuma bukaci a dakatar da biyan albashi da alawus-alawus ga daukacin ‘yan majalisar dattawan saboda yajin aiki jami’o’in, da kuma albashi da alawus-alawus na dukkan mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) har sai an saurari tare da tantance karar da ke gaban kotun.
KARANTA KUMA: Kungiyar Dalibai Ta mayarwa Da Ministan ilimi Martani
Ta ce, “Yayin da mai nema da dubban takwarorinta a duk fadin tarayyar kasar nan ke yawo kan tituna cikin bacin rai, wadan su kuma da mambobinsu na ci gaba da karbar albashinsu na wata-wata, alawus-alawus, rabo da sauransu ba tare da damuwa ba.
“ Sanin kowa ne cewa mafi yawan yaran da ke cikin manya a cikin al’umma da suka hada da ‘ya’yan ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati a Najeriya, suna zuwa makarantu masu zaman kansu ne kawai ko kuma yin karatu a kasashen waje.
Don haka ta bukaci kotun da ta dakatar da ayyukan Shugaban Majalisar Dattawa, Shugaban Majalisar Wakilai, Tattara Haraji, hukumar kula da kasafin kudi (RMAFC), Kwamitin Bayar da Kudi na Tarayya (FAAC), Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan shari’a, babban mai shari’a na jihar Abia da wasu jihohi 35 na tarayya, da mataimakin shugaban jami’ar Abuja.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Ba a sanya ranar da za a sauraren karar ba.
A wani labarin kuma: Mutane 6 Sun Rasu, Yayin Da Mutum 8 Suka Bata A Wani Hatsarin Jirgin Ruwa
Rahotanni sun bayyama cew mutane shida sun mutu a wani kogi bayan da jirgin ruwan da suke tafiya a ciki ya kife a kusa da kauyen Fada da ke karamar hukumar Guma a jihar Benue.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, SP. Catherine Anene, ta fada a ranar Alhamis cewa lamarin ya faru ne da karfe 1:00 na ranar Talata.