Matafiya sun makale a kan titin Legas zuwa Ibadan yayin da daliban da ke zanga-zangar yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yi suka tare hanyar a ranar Talatar nan.
Daruruwan Dalibai a karkashin kungiyar dalibai ta kasa (NANS) sun dakatar da zirga-zirgar ababen hawa.
Daliban karkashin jagorancin shugaban kungiyar NANS reshen jihar Ogun, Simeon Damilola, daliban sun taru ne a titin Redeem inda suka tare bangarorin biyu na babbar hanyar inda suka hana zirga-zirga a ciki da wajen Legas.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Matafiya da yawa sun makale a cikin dogon gosulo kuma an dakatar da harkokin kasuwanci na sa’o’i bayan zanga-zangar.
Karanta kuma: Daliban Jami’a Sun Shiga Zanga-zangar NLC
An kama ayarin wani fitaccen basaraken gargajiya a yankin Kudu maso Yamma, Olowu na Kuta, Adekunle Makama Oyelude, Tegbosun III a wajen zanga-zangar.
Sarkin wanda ya yi jawabi ga kungiyar daliban ya bukace su da su bude babbar hanyar domin tabbatar da zirga-zirga cikin walwala tare da yin alkawarin daukar matakin da hukumomin da abin ya shafa.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta warware rikicin da ya kunno kai ba tare da bata lokaci ba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Da yake magana a madadin Daliban, Simeon ya koka da abin da ya bayyana a matsayin mutuwar manyan makarantu a kasar bayan yajin aikin.
“Babu wata fa’ida a yi gardama kan wanda ke da laifi ko abin da za a yi. A bayyane yake cewa masu mulki ba su da kudin ilimi kuma gwamnatin Buhari ta gaza wajen alkawurran da ta dauka na inganta ilimi.
“Kamar yadda yake a yau, babu wata babbar jami’a a Najeriya da ta kai matakin duniya! Duk da haka, waɗanda ake kira ma’aikatan gwamnati suna tafiya ko’ina cikin duniya suna kashe biliyoyin don tura ‘ya’yansu kasashen waje don karatu.
“A matsayinmu na manyan masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, mu ne za mu iya ceton kanmu. Malaman mu suna fama da wahalhalu da rashin ci gaban da muke fama da su,” inji shi.
Yayin da aka ci gaba da kulle-kullen, mai magana da yawun hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) a jihar, Florence Okpe, ta shawarci masu ababen hawa da su yi amfani da wasu hanyoyin da za su bi domin ka da su hada babban gosulo.
A wani labarin kuma: Rashin Tsaro: Gwamnonin Arewa Da Sarakuna Sun Bukaci A Kafa ‘Yan Sanda Jiha
Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa na neman a kafa ‘yan sandan jihohi domin tunkarar kalubalen tsaro a yankin da ma kasa baki daya.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ce taron da aka gudanar a Abuja a daren ranar Litinin din nan ya duba matsalar tsaro a yankin Arewa da sauran al’amuran da suka shafi ci gabanta tare da kuduri aniyar tallafa wa gyaran kundin tsarin mulkin kasar domin ya dace da kafa ‘yan sandan jihohi.