Nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da sabon tsarin sufuri a cikin babban birnin jihar.
Manajan daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA Mista Baffa Babba-Dan’agundi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan yajin aikin da masu tuka keken mai kafa uku suka fara a jihar.
“Gwamnati za ta kaddamar da sabon tsarin sufurin ne saboda muna son a duba yadda ake tafiyar da harkokin sufuri kamar yadda ake yi a yanzu.
“Tuni dai shirye-shirye sun yi nisa, inda ya kai ga samar da ababen hawa.
“Masu yin amfani da babur Adaidaita sahu sun tafi yajin aiki saboda shigar da takardar izinin aikk. Gwamnatin jihar ta rage kudin daga N100,000 zuwa N8,000, domin samun damar biya.
“Duk da cewa wasu sun biya, wasu kuma ba sa son biyan kudaden shiga na gwamnati, kuma doka ta ce su biya.
“Ba sa son mutunta doka, suna ganin tsaron da suke samu ba don komai ba ne.
“Ba ni da wani ikon cewa dole ne su koma aiki.
“Duk da haka, ba su da wata hurumi da za su ce mini kada in nemi bayaninsu kuma kada in kama su da daukar matakin da ya dace a kansu,” inji shi.
Babba-Dan’agundi ya ce gwamnati ta damu da tsaro ba wai batun kudaden shiga ba.
“Wasu daga cikinsu suna ci gaba da aikata laifuka tare da masu adaidata sahu, ba sa son yin rajista,” in ji shi.
Ya kuma ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci hukumar da ta taimaka wa wadanda wasu ‘yan baranda suka lalatawa baburan mai kafa uku a lokacin da suka yanke shawarar kin shiga yajin aikin.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa fasinjojin sun makale a Kano ranar Litinin bayan yajin aikin mako guda da masu tuka babur ansuka shiga.
NAN ta ruwaito cewa lamarin ya rage cunkoson ababen hawa da aka saba samu a cikin garin sakamakon yawaitar babura mai kafa uku.
Yawancin fasinjojin ba a bar su ba tare da wani zaɓi face ko dai su dakatar da tafiye-tafiye na cikin gida a cikin babban birni ko tafiya a kafa ko kuma hawa motar kurkura. (NAN)