A ranar Litinin ne rundunar sojin Nijeriya suka kaddamar da shirin bukatar taya su da addu’a da neman komawa ga Allah domin ganin an kawo karshen rikicin Boko Haram.
Rundunar sojin sun shirya taro mai taken; “Countering Insurgency and Violent Extremism in Nigeria through Spiritual Warfare”, wato ma’ana kawo karshen ta’addanci da tsattsauran ra’ayi ta hanyar addu’o’i da komawa ga Allah.’ Wanda sashen cibiyar Resource ta Sojin ta shirya a Abuja.
Daraktocin sojin na gamayyar addinin Kiristanci da Musulunci ne suka shirya taron.
Shugaban Hafsan sojin, Tukur Buratai wa da Mohammed Yusuf ya wakikce shi, shi ne ya fara bude taron da jawabi.
Burutai ya ce akwai bukatar idan ana son kawo karshen ta’addancin Boko Haram a Nijeriya, sai an wayar da kan al’umma da kuma yakar tunanin da akidar masu ta’addanci. Domin a cewarsa akidar ta su ke sanya koyaushe suke da da kyankyasar wasu membobin.
A cewarsa idan har ba a kawo karshen akidarsu ba, ta’addanci zai ci gaba.