Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta tabbatar da killace gidan shugaban hukumar kula da harkokin kwallon kafan Nijeriya wato NFF a takaice. A wani bayanai da suka fitar a shafinsu na Twitter a ranar Juma’a.
Inda ta tabbatar da cewa ta killace gidan Amaju Pinnick shugaban NFF din ne dake Legas da kuma gidan mataimakinsa Shehu Dikko dake Abuja. Da kuma shugaban kamfanin LMC.
Har yanzu dai ICPC ba su yi karin bayani dangane da killace gidan ba. Amma rahotanni sun tabbatar da cewa ana zarginsu da cin hanci da rashawa.