Tun bayan da kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU ta sanar da Tsawaita yajin aikin da take zuwa nan da watanni uku dalibai a sassan Najeriya suka fara nuna kosawarsu a fili.
A jihar Oyo dalibai ne suka fito a babban birnin jihar wato Ibadan suna dauke da kwalayen kira ga mahukunta kan su kawo karshen zaman gidan da suke ba tare da zuwa makaranta ba.
Daliban dai sun fara zanga-zangar me daga wajen wani shakatawa na Trans zuwa sakatariyar gwamnatin tarayya, da Ikolaba, da Bodija, da Ojurin da wasu wurare na daban a Ibadan.
A jihar Osun Kuwa, nan ma haka abun yake domin kuwa daliban Jami’ar Obafemi Awolowo dake jihar Osun, ne suka fita zanga-zangar, wadda suka fara daga bakin makarantar tare da wasu kungiyoyin dalibai da suka mara musu baya.
Ita kuwa kungiyar daliban jami’ar Ajasin dake Akoko a jihar Ondo, sanar da shirin fita zanga-zangar sukai a ranar juma’a mai zuwa.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Ogunsanmi ya ce suna kara tunatar da daliban domin kasancewa cikin shiri.