Daga: Abbas Yakubu Yaura
Najeriya za ta samar da iskar gas ga kungiyar Tarayyar Turai (EU) yayin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine da aka fara a karshen watan Fabrairu.
Tawagar EU a Najeriya da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ne suka bayyana hakan a karshen mako.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/majalisar-%c9%97inkin-duniya-ta-ba-najeriya-umarnin-sakin-nnamdi-kanu-kuma-ta-biya-shi-diyya/
Mataimakin Darakta-Janar, na sashen Kula da Makamashi, Hukumar Tarayyar Turai, Matthew Baldwin ya yi wa manema labarai karin haske a Abuja.
Baldwin ya je Najeriya ne domin ganawa da jami’an gwamnati da ‘yan wasa masu zaman kansu, ciki har da masu ruwa da tsaki a fannin makamashi.
Jami’in ya yarda cewa Turai na cikin tsaka mai wuya, bayan yakin rashin kwanciyar hankali a kasuwar iskar gas da kuma barazanar katse samar da iskar gas.
“Mun kaddamar da aikin dandali na makamashi kuma burin farko shine mu kai ga amintattun abokan aikinmu kamar Najeriya don maye gurbin iskar gas daga Rasha”, in ji shi.
Kungiyar EU ta shawarci kasashe mambobin kungiyar da su rage yawan iskar gas da kashi 15 cikin 100 yayin da ta yi gargadin cewa za a iya dakatar da wadatar da Rasha gaba daya.
A Wani Labarin Kuma Wasu Ƴan bindiga sun afka gidan wani kansila a Jihar Adamawa inda suka kashe shi.
Ƴan bindigan sun shiga gidan Honarabul Ishaya Bakano ne a daren ranar Juma’a wayewar garin Asabar a Ƙaramar Hukumar Song inda suka harbe shi.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda reshen Jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce bayan an harbi kansilan an garzaya da shi asibiti amma rai ya yi halinsa.
DSP Yahaya ya kuma tabbatar da cewa ƴan bindigar sun harɓi ɗaya daga cikin ƴaƴan kansilan wanda yanzu haka yake jinya a asibiti.
Kafin rasuwarsa, Honarabul Ishaya ya kasance kansila mai wakiltar mazaɓar Gudu Mboi da ke Ƙaramar Hukumar Song ta Jihar Adamawa.