Kwana daya kafin nan, gwamnatin Habasha ta ce ‘yan kabilar Tigray na fadada fadan da ake gwabzawa a kan iyakokin kasar da Sudan.
Tun da farko, An kasashen duniya sun sha yin kiraye-kirayen kawo karshen sabon rikicin da ya balle a kasar..
Sai dai fadan na kasar Habasha ya bazu zuwa bangarori da dama, a makon da ya gabat, tun bayan wargajewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, domin kai kayyakin jin agaji a wasu sassan da lamarin ya shafa.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Atiku Ba Zai Zama Mai Kama-Karya Ba Idan Aka Zabe Shi – Okowa
Wani babban jami’in a dakarun mayakan Tigray ya fada a shafinsa na Twitter cewa an kaddamar da sabbin hare-haren ne a kansu daga bangarori hudu dake sassan yankin.
Sai dai kafar yada labarai ta BBC ta ce, Amma ba zai yiwu a tabbatar da wadannan ikirari ba, Saboda gwamnatin Addis Ababa ba ta ce uffan ba.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce, A halin da ake ciki, ana ci gaba da fargabar sake barkewar tashin hankalin a wasu sassan kasar.
Bangarorin biyu dai sun ce za su yi maraba da cimma matsaya ta lumana kan yakin basasar Habasha amma hakan bai hana cigaba da baiwa hammata iska ba.
A gefe guda Kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara na daga cikin wadanda harin ya rutsa da su a lokacin da aka yi ruwan bama-bamai a kauyuka a Afar, dake gabashin yankin na Tigray .
A WANI LABARIN KUMA: Za Ka Iya Naɗa Yusuf A Matsayin Gwamnan CBN – HURIWA Ga Buhari Kan Nadin Sirikin Sa
Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Najeriya, HURIWA, ta yi fatali da nadin Ahmed Halilu, yaya ga Uwargidan Shugaban kasa, Aisha Buhari, a matsayin Manajan Darakta na hukumar Buga kudi da muhimman takardu NSPMC.
HURIWA ta ce mai yiwuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karya rantsuwar da aka yi wa shugaban kasar Najeriya idan rahoton ya tabbata.