A daran Litinin ne, wasu ‘yan bindiga a kan babura guda biyar suka mamaye kauyen Illo da ke cikin karamar hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, wato NAN, ya bayyana cewa, ‘yan bindigar su na da rike da bindigogi daban-daban, inda su ka dunga harbe-harbe a sama tare da tursasa wa mazauna kauyen guduwa domin tsira da rayukansu.
NAN ya kara da cewa, ba a samu wanda su ka jikkata ba ko kuma asarar rayuka, amma lamarin ya tursasa wa mazauna kauyen guduwa zuwa wasu garuruwa da ke makwabtaka da kauye.
Lokacin da aka tuntubi shugaban karamar hukumar Bagudo, Alhaji Muhammad Kaura, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa lamarin ya auku ne ranar Lititin da misalin karfe 11.30 na dare.
“Wannan shi ne karo na farko da ‘yan bindiga su ka mamaye yankin, amma babu wani da ya kai rahoton lamarin ga hukumomin tsaro.” Kaura ya cigaba da cewa, daga baya ‘yan bindigar sun kewaye garin.
Ya ce, lokacin da kungiyar ‘yan sa-kai tare da mazauna kauyen su ka fuskance su, sai su ka fara harbe-harbe. “Daga baya mazauna kauyen sun gudu domin tsira da rayukansu. “Babuwa wani wanda su ka yi garkuwa da shi ko kuma su ka kasha a cikin wannan lamari.”
Shugaban karamar hukumar ya bukaci mazauna yankin da ku kai rahoton duk wani mummunar lamarin da su ka gani a yankinsu.
A halin yanzu an shawo kan lamarin, inda mutane sun cigaba da gudanar da ayyukansu yadda su ka saba.” Lokacin da manema labarai su ka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, DSP Nafiu Abubakar, a kan lamarin, sai ya ce, zai tuntube su daga baya.