Rahotanni daga jihar Kaduna na nuni da cewa wadansu ‘yan bindiga sun farmaki wata makaranta inda suka yi awon gaba da da dalibai har guda bakwai da kuma wata Malama guda daya bayan sun kashe wani magidanci.
Majiyarmu ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na safiyar jiya litinin ne ‘yan bindigar suka farmaki makarantar mai suna Prince Academy a kauyen Damba-Kasaya cikin karamar hukumar Chikun na jihar Kadunan lokacin da dalibai ‘yan aji 3 ke gab da fara zana jarabawa kamar yadda gidan rediyon Faransa suka labarto.
Rahotanni sun bayyana cewa; daliban na cikin wadanda gwamnatin Nijeriya ta yi umarnin su koma makarantu domin rubuta jarabawa.
Jaridun Nijeriya sun bayyana sunan malamar da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da ita a matsayin Christianah Madugu inda a bangare guda aka bayyana wanda ‘yan bindigar suka kashe a matsayin Benjamin Auta.
Wani matashi Akila Barde da ke shaidawa manema labarai yadda lamarin ya wakana ya ce ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne haye a babura.
Bayanai sun ce ilahirin daliban shekarunsu ya fara daga 12 zuwa sama yayinda suka kunshi mata da maza.