Hukumar Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Sokoto, ta karyata labarin da ke cewa, an rufe makarantar saboda barazanar tsaro a kwalejin.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban Kwalejin Ibrahim Uba ta ce, babu irin wannan barazanar da aka samu daga kowane bangare na kungiyoyin tada kyar baya.
Sanarwar ta ce “Domin fayyace gaskiyar lamari, a ranar Litinin din data gabata, an kawo wasu dalibai 13 kwalejin daga Birnin Yauri, sakamakon mummunan abin da ya faru a makarantar su watanni da suka wuce, inda ake da niyyar mayar da su gidajen Iyayen su. ”
Sanarwar ta ce, “Amma kwalejin ta sami damar sanar da al’umar dake Makarantar cewa, babu irin wannan wasikar da aka samu daga yan Yan bindiga ko wani gungun masu aikata laifuka, ko kuma barazanar tsaro ga makarantar ta kowani bangare,” inji sanarwar.
KARANTA WANNAN LABARIN: An kashe yan Nigeria 693 a watan Agustan, inji WANEP
Sanarwar ta kara da cewa, hukumar gudanarwar Kwalejin, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da kuma hukumomin tsaro, sun yanke shawarar rufe makarantar don dakile tashin hankali, tunda tuni dalibai suka kammala jarabawar su, wanda ke nuna karshen wannan zaman.
Kazalika sanarwar ta kara da cewa, Kwalejin na tuntubar hukumomin tsaro dangane da tsaron rayuka da dukiyoyin dalibai, da na ma’aikatan.
Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, wasu mutane na daban, sun aika da sakonnin kartakkwana, suna cewa, Al’uma su je su dauki yaransu daga makarantar, saboda wasika daga yan bindiga dake barazanar kai wa Kwalejin hari.
A wani labarin Kuma na daban.
Kungiyar Marubuta Wasanni ta Kasa reshen Jahar Katsina, ta taya Ma’aikatar Kula da Harkokin Wasanni ta Jahar murnar kaddamar da Mambobin Hukumar gudanarwa na Kungiyar Kwallon Kafa ta Katsina United, gami da na Hukumar bada a gajin gaggawa ta Jaha.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar na Jaha Kwamared Nasir Sani Gide ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta bayyana nada Alhaji Muhammad Daha Umar Faruq a matsayin Shugaban Hukumar gudanarwa na Kungiyar Kwallon Kafa ta Katsina United a matsayin wanda ya dace, ta la’akari da dumbin gudunmuwar daya bayar domin cigaban harkokin wasanni a Jahar.
Sanarwar ta kuma yaba da kokarin Gwamna Aminu Bello Masari daya nada nagartattun mutane wanda zasu jagoranci Hukumar, inda yayi nuni dacewa hakan babu kokwanto zai taimakawa Ma’aikatar wasanni wajen ciyarda harkokin wasanni a matakin gaba.
Shugaban Kungiyar ya Kuma yabawa Kwamishinan wasanni Sani Aliyu Danlami daya ke jajircewa wajen cigaban harkokin wasanni a Jahar.
Sanarwar ta kuma bukaci Sabbin Shuwagabannin Hukumar gudanarwar, da su taimaka wajen bada shawarwari dazasu taimakawa Ma’aikatar ta gudanar da harkokin ta yadda ya kamata.
Comments 1