Daga Muhammad Muhammad
Rahotanni da ya fito daga jihar Zamfara sun tabbatar da cewa; an samu karin ‘yan bindiga da suka tuba inda suka mika tarin makamai da suka hada da bindigogi da alburusai, da kuma kakin soja, ga jami’an tsaro.
Yayin tabbatar da tuban gungun ‘yan bindigar, Kakakin rundunar ‘yan sandan Zamfara Muhammad Shehu, ya ce lamarin wani bangare ne na ci gaba da aiwatar da shirin kawo karshen tashin hankalin hare-haren ‘yan bindiga a jihar ta hanyar sulhu, a karkashin jagorancin gwamnati da Sarakunan gargajiya.
A watannin baya, Zamfara ke kan gaba tsakanin jihohin arewa maso yammacin kasar dake fama da hare-haren ‘yan bindiga da kuma satar mutane son karbar kudin fansa, sai dai a halin yanzu rahotanni sun nuna cewa an samu saukin matsalar tsaron a jihar ta Zamfara, biyo bayan yarjejeniyar sulhun da aka kulla da ‘yan bindigar.
A baya-bayan nan gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa, mutane dubu 1 da dari 4 da 60 ne suka rasa rayukansu a hare-hare har guda 330 da ‘yan bindiga suka kaddamar a cikin watanni bakwai da suka gabata, musamman a yankunan Arewa maso yammacin kasar.