Yan Bindiga Sun Ƙaddamar da Munanan Hare-hare a Ƙananan Hukumomi 3 Na Jihar Katsina
‘Yan bindiga suna ci gaba da mayar da rayuwar mazauna jihar Katsina cikin wani mummunan hali, inda suka kai hare-hare da dama a fadin jihar cikin sa’o’i 72 da suka wuce.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Sabuwa: Ƴan Najeriya a duk jihohin Najeriya sun yarda da Peter Obi da LP — Ozigbo
A hare-haren da aka kai tsakanin Alhamis da Asabar, an sace wasu yara yayin da aka kashe iyayensu.
A ranar Asabar da daddare wasu ƴan bindiga kimanin 20 suka kai farmaki garin Bakori inda suka yi awon gaba da ƴan uwa 7 na wani Malam Muntari Samuru, wanda aka yanke shi da Adda.
A cewar wani Mohammed Sani, an kai harin ne da misalin karfe 8:15 na dare lokacin da akasarin mutane ke gudanar da Sallar Isha’i a gidan wanda abin ya shafa a bayan Asibitin Bakori.
Kafin kai harin, ƴan bindiga sun kashe Malam Hamisu Barebari daya tare da yin garkuwa da mutane bakwai da suka hada da mata.
“’Yan fashin sun yi ta laɓe ne a gonakin da ke kusa da su, kafin su bugi wata mata a kan hanyarta ta kai niƙar masara a Bakori; Suka yi mata duka suka kashe ta. Uku daga cikin Mutane Bakwai da suka sace sun yi nasarar tserewa zuwa gida,” Umar Barebari, cewar wani mazaunin garin.
A daren ranar Alhamis ne ‘yan fashin suka kai farmaki kauyen Kurami dake kan titin Funtua zuwa Bakori da misalin karfe 8:00 na dare inda suka tafi tare da yara uku.
Malam Umar Kurami, Mahaifin daya daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su, ya ce ƴan ta’addan sun tafi da yaronsa.
“Kamar mafarki ne ƴan fashin Dajin suka nuna min bindigu a gidana, suna neman kudi; da suka fahimci cewa ba ni da kudi, sai suka fitar da ni tare da yarona amma daga baya suka ce in je in nemi kuɗin fansar yarona,” inji shi.
A Ƙaramar Hukumar Danja, a lokaci guda ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan Majema da Tashar Gero da ke yankin Tandama a ranar Juma’a.
Sun kashe Malam Isah Majema tare da sace ‘ya’yan Alhaji Wada guda uku.
Ƙauyukan Danja, Bakori da Funtua suna rayuwa cikin firgici, kamar yadda majiya ta bayyana.
Hankali ya tashi sakamakon hare-haren da suke kai wa a kai a kai daga karfe 6:00 na yamma zuwa karfe 4:00 na safe.
Gambo Isah, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Katsina, ba’a samu kiran wayar da ba, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
A wani labarin kuma:Kar ku raba Mana Najeriya da Addini – Olawepo-Hashim ga Ƴan Siyasa
Wani Jigo a Jam’iyyar APC Kuma Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Peoples Trust a Zaɓen 2019, Gbenga Olawepo-Hashim, a ranar Lahadi, ya gargaɗi ƴan siyasa kan kara karfafa ɓaraka a kasar nan domin cikar burin su na 2023.
Don haka, yayi gargaɗin cewa”al’umma ba za ta iya yin watsi da wannan tsarin Dimokuraɗiyya a kan son kai na Ƴan Siyasa da ke kan manufa na kishi da girman kai.”