Wasu ‘yan bindiga a ranar Juma’a sun kashe mutane akalla 13 a wani hari da suka kai a wani masallaci a unguwar Ruwan Jema da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara, yayin da ake tsaka da gudanar da sallar Juma’a.
Harin ya zo ne makonni uku da sace wasu masu ibada 44 a wani masallaci da ke unguwar Zugu a karamar hukumar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Komawa Ga Noma Ne Mafita Ga Matsalar Najeriya – Buhari
Daga baya ‘yan bindigan sun sako masu ibadar kwanaki bayan sun biya kudin fansa naira miliyan biyar.
Al’ummar dake Garin Ruwan Jema, mai tazarar kilomita 15 gabas da garin Bukkuyum, hedkwatar karamar hukumar ta sha fama da munanan hare-hare a baya. Mazauna yankin sun kuma biya miliyoyin nairori ga ‘yan fashi a matsayin haraji.
Wani mazaunin garin Usman Lawal ya ce, “Lokacin da suka yi wa garin kawanya, ‘yan ta’addan dauke da makamai sun shiga masallacin ne a lokacin da masu ibada ke tsaka da sallar Juma’a. Muna Raka’a ta Karshe sai kwatsam suka fara harbe-harbe nan take tashin hankali da hargitsi ya barke yayin da kowa ke gudu don tsira da rayuwar sa.”
“Sun bude wa masu ibada wuta, inda suka kashe akalla mutane 13 a nan take. Wasu da dama kuma sun jikkata a turmutsutsu. ‘Yan ta’addan sun kuma kashe wasu mazauna yankin da suka samu a cikin dazuzzukan da ke kewaye. Ana dibar gawarwakin mutanen ne daga gonakin kuma an shirya sallar jana’izarsu a yau.”
“Ana ci gaba da tsintar gawarwaki daga dajin. Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su na karbar magani a cibiyoyin kiwon lafiya a Zamfara da kuma jihar Sokoto da ke makwabtaka da ita.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, bai amsa kiran da wakilinmu ya yi masa ta wayar salula ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
A wani labarin kuma, Ganduje Ya Taya Masarautar Saudiyya Murnar Cika Shekaru 92
Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya taya masarautar kasar Saudiyya murnar cika shekaru casa’in da biyu da dunkulewa a matsayin masarauta.
Ganduje Ya bayyana haka ne wajen taron bikin murnar hadewar masarautar da ya gudana a dakin taro na The Afficent dake jihar Kano, wanda ofishin jakadancin kasar ta Saudiyya dake jihar nan ya shirya a yau Asabar.