Yan bindiga sun kone gidan kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Nasiru Muazu Magarya , da wasu gidajen mazauna unguwar dake karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara.
Shugaban kwamitin tsaro da yaki da yan bindiga a jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Litinin.
Inda ya ce yan bindigar sun mamaye garin, kuma sun kona wasu gidaje, ciki har da na kakakin majalisar dokokin jihar.
A cewarsa, hakan na zuwa ne sakamakon ci gaba da kai farmaki da sojoji ke yi kan Yan bindiga a karamar hukumar Zurmi dake jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi awon gaba da Matan aure a Abuja
Shugaban kwamitin, wanda ya ziyarci al’ummar da abin ya shafa don duba halin da’ake ciki a yankin, ya ce, gwamnati na kokarin bayar da tallafi ga wadanda lamarin ya shafa, tare da tura karin jami’an tsaro don kare jama’a yankin baki daya.
Duk da cewa, bai bayyana ko an rasa rayuka ba a yayin farmakin da Yan bindigan suka kai, amma ya ce, an yi nasaran kama masu samar da abinci, man fetur da sauran kayayyaki ga yan ta’addan.
Kazalika Shugaban kwamitin ya ce, wadanda ake zargin sun yi amfani da kwale -kwale wajen dauko kayayyakin daga jihar Sokoto, inda suke kokarin kai wa yan bindiga a karamar hukumar Shinkafi dake jihar Zamfara.
A karshe ya kuma kara da cewa, an mika kayayyakin abincin da masu samar da Man ga Yan bindiga, zuwa wurin jami’an rundunar yan sanda, domin ci gaba da gudanar da bincike.
A wani labarin Kuma na daban
Shugaban Kwamitin Majalisar Dokoki ta Kasa akan hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi Francis Ottah yace zai gabatar da wani kudiri dazai sanya Hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi ta rika yin gwajin Kwaya lokaci zuwa lokaci, ga duk Wanda ke neman kujerar siyasa a Najeriya.
A cewar sa kudirin zai Kuma baiwa Hukumar damar gudanar da gwajin kwaya ga Jami’an tsaro, gami da Daliban dake neman guraben karatu a Manyan Makarantun Najeriya ya zama dole sai anyi masu gwajin Kwaya.
Dan Majalisar a jawabin daya fitar a ranar Litinin a tabakin mai taimaka masa akan Kafafen Yada Labaru Andrew Agbese, yace illolin kamuwa da cutar Shan miyagun kwayoyi ya fantsama a dukkanin bangarori na Al’umma, kuma gwajin Kwaya ne kadai zai iya wayarwa mutane Kai akan matsalar dake tattare da shan miyagun kwayoyin.
Ya bayyana cewa, yadda wasu Yan siyasa ke canja halayyar su gami da yawaitar ayyukan ta’addanci da ake yi a cikin Al’umma dukkanin su kwaya ce ta haifar su.
Ya jaddada cewa, za’a iya magance hakan idan ya zaman to wadanda suke fama da matsalar basa cikin masu Shan miyagun kwayoyi.
“Ina gabatar da kudiri dazai baiwa Hukumar Hana Shan miyagun kwayoyi ta Kasa, damar gudanar da gwaji ga dukkanin yan siyasa, da manyan ma’aikatan gwamnati, da Sojoji da sauran Hukumomin tsaro, gami da Matasa masu neman guraben karatu a Manyan Makarantun Kasa. Wannan zai kawo karshen hauka da ake yi a bangarorin gami da wayar wa Al’umma kai.
“Shan miyagun kwayoyi abune wanda ya mamaye ko’ina a cikin Al’umma, daga Makarantun Sakandire zuwa Jami’o’i, daga Arewa zuwa kudu, daga Yan siyasa zuwa Ma’aikatan Gwamnati. A takaice Najeriya itace kasa data fi kowace yawan masu Shan miyagun kwayoyi, kuma Tabar wiwi ita tafi yawaita a Kasar,”inji shi.