Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a garin Maisamari da ke karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba, inda suka kashe wani hakimi mai suna Alhaji Abdulkadir Maisamari.
Shaidu sun ce an kashe Maisamari ne a lokacin Sallar Isha’i a daren ranar Litinin.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun bude wuta ne nan take suka kutsa cikin masallacin.
An kuma bayyana cewa, mazauna garin sun yi tir da harin yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa wani dutse da ke kusa da garin.
Wani mazaunin garin mai suna Musa Sale ya shaida wa jaridar Daily trust cewa wasu jajirtattu ne suka tunkari ‘yan bindigar da suka gudu da karfi.
Ya ce ba a sace kowa ba, kuma an yi jana’izar Hakimin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Lamarin na Maisamari ya kawo masallatan uku da aka kai hari a jihar Taraba a makonnin da suka gabata.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayar da cikakken bayani ba