Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga wadanda ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun bude wuta akan wasu bayin Allah Masallata dake sallar Tahajjudi na karshen watan Ramadan a birnin Maiduguri.
Majiyarmu ta YERWA EXPRESS NEWS ta bayyana cewar wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar ‘yan Bindigar sun bude wuta akan bayin Allah Maza da Mata da ke gudanar da ibada Tahajjudi a babban masallacin Sajeri dake kwanar Ajilari dake birnin Maiduguri a daren jiya Juma’a.
Mazauna yankin a halin yanzu sun kauracewa gidajen su domin neman tsira da rayukansu daga farmakin ‘yan Ta’addan.
Har kawo ya zuwa yanzu dai babu wani rahoto na adadin wadanda suka rasa rayukansu ko suka ji rauni a sakamakon harin Ta’addanci.
Hakazalika babu wata magana da aka samu daga bangaren rundunar soji da ke yaki da ‘yan ta’adda a Maiduguri dangane da harin, a bangaren rundunar ‘yan sanda ma babu wani bayani da ya fito duk da kokarin da aka yi na ji daga gare su.