Yan bindigan da sukayi garkuwa da mutane a yankin Maza-Kuka da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja sun bukaci iyalan wadanda abin ya shafa su biya Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa.
Wasu ‘yan bindiga sun dai mamaye al’ummar garin ne da sanyin safiyar ranar Litinin a lokacin da mutanen kauyen ke gudanar da sallar asuba, inda suka kashe mutane akalla 18 tare da yin garkuwa da wasu da dama.
Wata majiya daga al’ummar da ta yi magana, ta shaida wa wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa, an yi garkuwa da mutane 11 ciki har da babban Limamin garin.
“Sun kira waya jiya, inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 60.” Inji majiyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun harbe wani Matashi Har Lahira a Imo
“Ba mu san abin da za mu yi ba a yanzu. Ko da yake masallacin Juma’a ne, an yi garkuwa da babban limamin da ke jagorantar salloli biyar tare da wasu mutane 10,”
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wata mace na cikin wadanda aka kashe a harin.
Wani Mutum garin ya tabbatar da cewa, matar mata ce ga babban abokinsa,“Lokacin da suke kai hari, sai ta yi ihu da yunkurin gudu Wanda hakan yasa suka harbe ta kuma ta mutu nan take.” Inji shi
“Idan ba haka ba, ba su taba mata ba, kuma duk wadanda aka sace maza ne” a cewar shi.
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamnonin yankin kudu masu kasar nan a jiya talata, sun yi wata ganewa a jihar Legas domin lamura da suka shafi tsaro da kuma dangogin su a yankin.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ne ya jagoranta taron wanda ya gudanar a fadar Legas dake garin Marina a jihar.
A dai karshen taron wanda aka shafe tsawon lokaci a na ayyuka, Gwamna Akeredolu yace, daga cikin dalilan da suka shafi dan gane da matsalar tsaro a yankin, sun hada da damuwa da za abi domin matsalar.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da mai masaukin baki Gwamna Babajide Sanwo-Olu, da gwamnan Osun Gboyega Oyetola, da Dapo Abiodun na jihar Ogun, da kuma Kayode Fayemi na jihar Ekiti.
Sai dai duk da cewa, gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo bai halarci taron ba, amma ya sami damar nunasa Rauf Olaniyan.
Kazalika bayan taron tattaunawan sun kuma ziyarci jigon jam’iyar APC na kasa Bola Tinubu, wanda bai jima da dawuwa daga kasar ba domin duba lafiyar sa.