Ayarin Honorabul Chris Emeka Azubogu, dan majalisa mai wakiltar mazabar Nnewi ta Arewa da ta Kudu na mazabar Ekwusigo a majalisar wakilai, ya fuskanci harin bindiga a jihar Anambra a yau Alhamis.
An harbe direban dan majalisar har lahira, a sanadiyar Kai harin na yan bindigan.
Azuogbu wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jiya Laraba, baya cikin ayarin lokacin da maharan suka kai harin.
Mai magana da yawun dan majalisar Ikechukwu Onyia, ya tabbatar wa da manema labarai afkuwar lamarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun Bankawa Ofishin Yan sanda Wuta a Anambra
Ana samun tashin hankali a Anambra, a yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 6 ga watan Nuwamba shekarar 2021.
Ko a ranar Talata da ta gabata, an kashe Dr Chike Akunyili Mijin matar tsohowar Daraktar na Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC da rana.
An kashe shi tare da wasu mutane bakwai a jihar.