Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari fadar sarkin Kagara da ke karamar hukumar Rafi a jihar Niger.
Kuma yan bindigan sun kai hari a kasuwar Kagara da misalin karfe 6 na yamma. lokacin da aka rufe kasuwar, inda ukai ta yin harbi ba zato ba tsammani don tsoratar da mutane yankin.
Yan bindigar sun mamaye garin akan babura kusan 20, tare da goyon mutane uku akan kowane babur.
Yan kasuwar sun watsar da kayayyakin su domin gudun neman tsira da rayukansu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NCSDC ta kama Mutane 4 kan zargin Saffarar Gurbataccen Mai a Anambra
Mazauna Kagara kuma sun tsere cikin daji. Wasu sun hau tsauni don gudun kar a yi garkuwa da su ko a harbe su.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a Sami labarin rahoton mutuwa ba, ko na garkuwa da wani Mutum ba sanadiyar lamarin..
Rahotanni na nuna cewa, Sarkin Kagara Alhaji Ahmed Garba Gunna Attahiru baya cikin garin, lokacin da aka mamaye fadar sa.
Wasu majiyoyi sun shaida wa Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta wayar tarho cewa, ‘yan fashin sun mamaye garin ne ta hanyar makarantar firamare ta Attahiru zuwa hanyar Madaka, zuwa cikin daji, inda suka yi awon gaba da daliban Kagara watanni kadan baya.
Duk kokarin da Jaridar The Nation ta yi don Ji ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Niger, DSP Wasiu Abiodun don tabbatar da harin abun ya citira, saboda bai dauki wayarsa ba, kuma bai amsa sakon da aka aiko masa ba.