Wasu yan bindiga da ba a tantance su wanene ba sun farmaki Ministan sufurin kasar Uganda da kuma tsohon Kwamandar sojin kasar Janar Kutumba Wamala inda suka hallaka diyarsa gami da direbansa.
Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar wadanda suka zo a kan babura sun yi ta luguden wuta kan motar mamatan a kusa da gidan su dake birnin Kampala.
Shugaban kasar ta Uganda Yoweri Musseveni ya tabbatar da cewa gwamnatin za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen zakulo makasan wanda ta alakanta su da yan ta’adda.
Yanzu haka jami’an soji na nan girke a harabar asibitin da ake yiwa Janar Wamala aiki, ko da yake an bayyana cewa yana nan ne rai a hannun Allah.