Yan bindiga sun kai farmaki garin Tangaza dake karamar hukumar Tangaza na jihar Sokoto, inda suka kashe Mutum biyu, tare da yin garkuwa da wasu yara hudu a yayin harin.
Sun kuma jikkata wasu mutane uku da a halin yanzu suke jinya a asibiti, yayin da aka yan bindigan suka kwashe kayayyakin abinci, lemun kwalba da dai sauran su a garin.
Wata majiya a garin da ta zanta da Jaridar Tribune Online ta wayar tarho, ta bayyana cewa, wadanda ake zargin masu Garkuwa da mutane ne, sun kaddamar da hare -haren ne bayan sallar Magariba a jiya Juma’a, sannan suka fara harbi ba kan Mai uwa da wabi, inda suka kashe wani mai shago nan take, da wata karamar yarinya data mutu a asibiti.
Ya kara da cewa, shiga tsakanin da jami’an tsaro suka yi tare da yan bangan yankin, ya samu nasarar kubutar da daya daga cikin wadanda aka sace, yayin da masu garkuwan suke kokarin su tsere wa da mutanen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Taliban ta ki amincce wa Mata su koma Makaranta a Afghanistan
Kazalika ya ce, “Sun kuma yi garkuwa da kananan yara kanana biyar, yayin da jami’an tsaro suka kubutar da daya daga cikinsu wadanda aka sace.” Inji shi.
Sai dai duk kokarin da majiyar jaridar Dimokuradiyya ta yi don Ji ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar yan’sandan jihar Sokoto ASP Sanusi Abubakar, ya citira har kawo hada wannan rahoton.
A wani cigaban Kuma.
Bayan shafe kusan wata guda a tsare Manjo Christopher Datong, wanda ‘yan bindiga suka sace daga gidansa a Kwalejin Tsaron Najeriya NDA da ke Kaduna, a ranar 24 ga Agusta 2021, ya shaki iskar ‘yanci.
‘Yan bindigar sun kai hari tare dayi garkuwa da Datong a babban sansanin sojoji da ke Afaka, Kaduna, bayan da suka kashe jami’anta biyu da aka bayyana sunayensu Laftanar Wulah da Flight Lieutenant Okoronkwo.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, yace nakalto Ezindu Idimah wani Kanal kuma Mataimakin Darakta, hulda da jama’a na runduna ta daya a Kaduna, wanda ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa cewa an kubutar da jami’in a ranar Juma’a, ya kara da cewa an lalata sansanin ‘yan ta’adda da yawa a yankin Afaka- Birnin Gwari yayin da aka kashe’ yan ta’adda da yawa yayin aikin ceton.
Bayan isa sansanin, sanarwar ta ce, ana zargin wurin da ake tsare da Datong, sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar kuma ana cikin haka ne aka ceto jami’in da aka sace, inda ya kara da cewa jami’in ya samu rauni kadan, amma An yi jinyarsa a wani asibiti kuma an mika shi ga NDA don ci gaba da aiki.
Idimah ya ce “Ayyukanmu za su ci gaba har sai mun kamo ko kuma mu kawar da maharan da suka kashe jami’ai biyu a cikin NDA a ranar 24 ga Agusta 2021,” in ji Idimah.
Comments 1