Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu masu ibada a wani masallacin Juma’a da ke unguwar Zugu a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun boye bindigunsu a cikin tufafin su, inda suka kutsa cikin masallacin a lokacin da Limamin zai fara gabatar da huduba.
An ce masu kutsen sun ce wadanda ke wajen masallacin su shiga ciki.
“Lokacin da suka yi wa masallacin kawanya, sai suka bukaci wadanda ke wajen da su shiga cikin masallacin, suka shaida wa masu ibada cewa, sun zo ne domin tattaunawa a sako wasu da aka kama musu.
KARANTA ANAN: Ganduje Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinoninsa
“An kuma sace wasu da suke wajen masallacin saboda ba su san cewa wasu ‘yan bindiga sun dauki mkamai a waje ba.
Yan bindigar dai Sun harba bindiga da dama sama sannan suka koma daji tare da wadanda suka yi garkuwa da su,” kamar yadda wani mazaunin garin da ya bayyana.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Muhammad Shehu ya ce bai samu rahoton harin ba amma ya yi alkawarin sanar da halin da ake ciki.