Shugaban kasar Burkina Faso Roch Kabore ya bayyana cewa wasu yan bindiga a kasar sun hallaka mutane sama da 100 a wani hari kan kauyen Solhan dake arewacin ƙasar.
Yayin dirar mikiya da sojojin suka yi a talatainin dare, sun kuma kona gidaje kurmus tare da kasuwanni a Kauyen.
Har kawo yanzu babu wani ko wata kungiya da ya dauki alhakin wannan hari.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa hare haren ta’addanci na ci gaba da karuwa a kasar, musamman a iyakarta da kasar Mali.
Kazalika a wani harin na ta’addanci a daren jiya yan ta’adda sun hallaka mutane sama da 15 a kauyen Tadaryat mai nisan kilomita 150 daga arewacin Solhan inda aka kai harin na yau.
Har ila yau a watan da ya gabata mutane 30 sun gamu da ajalinsu a wani harin da aka kai a gabashin kasar ta Burkina Faso.