Akalla mutane 65 wadanda akasari manoma ne rahotanni suka ce sun rasa rayukan su a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari a lokuta daban-daban a jihohin Katsina da Borno a tsakanin ranakun Lahadi zuwa Talata.
Wakilanmu sun tattaro cewa mutane 50 ne suka mutu sannan wasu da ba a tantance adadinsu ba sun jikkata lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari a karamar hukumar Kala Balge da ke jihar Borno a ranar Lahadi.
Kala Balge na daga cikin ƙananan Hukumomin yankin Gabas maso gabas kuma tana da hedkwatarta a garin Rann, wanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru mai tazarar kilomita 365 daga Maiduguri.
Rann da kauyukan da ke makwabtaka da su sun kasance wuraren da ‘yan ta’adda ke kaiwa hari, wadanda suka kashe da raunata mutane tsawon shekaru.
Al’ummar yankin wadanda galibinsu manoma ne, masunta da ‘yan kasuwa sun rasa ‘yan uwansu da dukiyoyinsu a hannun ‘yan ta’adda saboda karancin jami’an tsaro da kuma dawo da kungiyoyin farar hula.
A yayin kisan na ranar Lahadi, wata majiya ta shaida wa daya daga cikin wakilanmu cewa maharan sun zargi mutanen yankin da yi musu leken asiri tare da bayyana ma sojoji inda suke duk da gargadin da aka yi musu na su kalli wata hanya.
Har yanzu dai sojoji da gwamnatin jihar Borno ba su ce uffan ba kan lamarin.
A nasa bangaren, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Abdu Umar, wanda ‘yan jarida suka same shi a dakin taro na kasa da kasa, dake sakatariyar Musa Usman a Maiduguri, a jiya, ya ce baturan ‘yan sanda DPO bai yi masa bayani ba, balle wani mai fada aji a Yankin ko shugaban karamar hukuma.