Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa an kashe mutum uku daga Chadi wanda suka zo kasar Mali domin wanzar da zaman lafiya. Sun rasa rayuwarsu ne a daidai lokacin da wadansu ‘yan bindiga suka kai wa tawagar majalisar dinkin duniya harin bom a Arewacin Mali inda suka kashe mutum uku daga cikinsu tare da raunata da dama.
Kakakin majalisar dinkin duniya Stephane Dujarric, ya ce Babban Sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres ya yi tir da wannan hari da aka kai a Aguelhok dake yankin Kidal. Inda ya ce wannan harin na ta’addanci ne a karkashin dokokin duniya.