Wasu ‘yan bindiga sun harbe mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Aminu Umar a jihar Katsina.
Marigayin da tawagarsa an yi musu kwanton bauna ne a lokacin da suke aikin share fage a dajin Zakka da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina a ranar Talata.
Har ya zuwa rasuwar Umar shi ne kwamandan ‘yan sanda na yankin Dutsinma.
Majiyoyi a yankin Zakka sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan sanda da ‘yan bindiga sun yi arangama a wani kauye mai suna Yauni da ke gundumar Zakka a cikin garin Safana.
“Jami’an ’yan banga a nan sun shaida mana cewa za a samu hadakar tawagar ‘yan sanda tare da ‘yan banga daga Kurfi zuwa kauyen Yauni don fuskantar ‘yan bindiga kuma suka shiga cikin tawagar.”
“Daga baya mun ji an yi artabu da ‘yan sanda da wasu ‘yan banga da ‘yan bindigar suka harbe.
“Duk da haka, kimanin motocin sojoji bakwai ne suka bayar da tallafi a yankin; daga baya muka ga wasu motocin ‘yan sanda suna jigilar wasu gawarwakin amma ban iya tantance gawarwakin ba saboda ba na kusa da su,” inji shi.
(ACP) Aminu Umar, wanda ya biya farashi mai tsoka a wata arangama da ‘yan bindiga a jihar Katsina. Da yake tsokaci kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce Umar ya mutu ne a fadan da ‘yan sanda suka yi da ‘yan bindiga sama da 300.
Ya ce wani mutum guda ya mutu a lamarin, amma bai bayyana ko wane ne dayan da abin ya shafa ba.