A kalla mutane ashirin ne suka gamu da ajalinsu a karamar hukumar Wushishi sa kuma Lavun dake Jihar Neja yayin wani mummunar harin ta’addanci da ya auku a shekaran jiya Juma’a a Kananan hukumomin.
Baya ga wadanda suka mutu kuma akwai wasu da dama da suka jikkata wanda har yanzu ba a banance adadin su.
Galibin jama’a dake gudun ceton rai sun yi ta faɗawa ruwa insa ruwan yake cinye su, duk da haka ba su daddara ba domin an ce abinda ya kori ɓera ya faɗa wuta, lallai ya fi wutar zafi.
Majiyoyi da dama sun shaida cewa yan bindigar sun killace manyan hanyoyin yankin nan da ba sa rabuwa da jama’a wato Tegina zuwaa Zungeru zuwa birnin Minna inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi, tare da kashe mutane ciki har da mata da ƙananan yara.
Wannan lamari ya sa ala tilas waɗanda suka Kudirin anyar bin hanyar komawa da baya tare da gudu su bar ababen hawansu don samun saukin rayuwa.
Rahotanni sun ce wasu tsirarun yan sanda sun hallara a gurin da wannan mugun alkaba’i ya faru, to sai dai an ce Sarkin yawa ya fi Sarkin Karfi, wannan neya sa yan sandar su ma suka kama gabansu bayan ganin yadda yan bindigar suka yi fitar barden guza.