A kalla mutane bakwai ne suka gamu da ajalinsu yayin da kuma aka garkuwa da wasu mutane 10, biyo bayan harin wasu yan Bindiga kananan hukumomin Chikun da Kajuru da Giwa na Jihr Kaduna.
Mutane hudu daga cikin wadanda aka kashen an yi garkuwa da su a kauyen Tsohon Gayan dake karamar hukumar Chikun yayi da sauran biyu kuma aka hallaka su a kauyen Iri Station dake karamar hukumar Kajuru.
Wani mazaunin kauyen na Iri Station mai suna Moses Mathew ya shiada cewa yan bindigar sun shigo ne wuraren karfe daya na dare dauke da muggan makamai inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
Al’ummar wadannan yanki dai yanzu na ci gaba da kira ga gwamnatin jiha da ta taimaka ta kai musu ɗoki ta hanyar jibge musu jami’an tsaro.
A bangaren sa, Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Mista Samuel Aruwan ya tabatar da cewa gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kai musu agajin gaggawa.
A yan baya bayan nan dai yankin arewa maso yammacin kasar nan na fuskantar yawan matsalolin yan fashin daji, lamarin da yayi sanadiyar salwantar rayukan Mutane da dama tare da garkuwa da wasu.
Da ma dai gwamnatin jihar karkashin Mallam Nasir el-Rufa’i ta ce ba za ta tattauna da kowane dan bindiga, a wani mataki na ganin cewa an dakile matsalar sace sacen jama’a.