‘
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Jouro Manu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba, inda suka kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu shida.
Mazauna yankin sun ce maharan sun zo ne a kan babura da misalin karfe biyu na ranar Lahadi inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi
Mazauna yankin Umar Sa’idu da Abdullahi Mohammed sun shaida wa wakilin jaridar PUNCH cewa, jama’a na kauracewa al’ummomin da ke kewayen saboda tsoron kada a kashe su ko kuma a yi garkuwa da su.
Mukaddashiyar jami’iar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, Gambo Bajabu Kwache, ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Litinin , ta kuma ce tuni ‘yan sanda suka yawo kan lamarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanatan APC Ya Hassala Kan Matsalar Tsaro, Ya Buƙaci Babagana Monguno Ya Sauka
“Mun san halin da ake ciki. Mun tura jami’an mu yankin domin zakulo maharan,” inji ta.
Anashi bangaren Tsohon shugaban karamar hukumar Gassol, Honorabul Musa Chul, a shekarar da ta gabata ya yi tsokaci kan yadda ‘yan ta’adda suka sake yin sansani a dazuzzukan yankin karamar hukumar.
A wani labarin kuma na daban.
DR Congo Ta Kama Jami’an Sojin Majalissar Dinkin Duniya Kan Kan Zargin Kashe Fararan Hula
An kama Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Cango kan kisan fararen hula biyu a wani wuri dake kan iyakar kasar a jiya Lahadi. Kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Patrick Muyaya ya sanar
Rahotanni sun kuma bayyana cewa, wasu mutum 15 sun jikkata yayin da dakarun wanzar da zaman lafiyan suka kutsa kai cikin jama’a a hanyarsu dake iyakar kasar da Uganda.
Mista Muyaya ya ce gwamnati da tawagar jami’an wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, na gudanar da bincike kan lamarin.
Ya kara da cewa gwamnati na kira ga al’ummar Congo da su kwantar da hankulansu musamman wadanda ke yankin Kasindi da kuma daukacin lardin Kivu dake Arewacin kasar.