Ana fargabar an kashe mutum daya, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa ‘yan kasuwa a Ofeapo kan titin Idrisu-Bagana a karamar hukumar Omala ta jihar Kogi.
Daily Trust ta ruwiato cewa, Wani ganau ya bayyana cewa an yi wa ‘yan kasuwar kwanton bauna ne a yayin da suke komawa gida daga Kasuwar Bagana da misalin karfe 8:30 na daren ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fasinjoji 20 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Mota
An ruwaito cewa, ‘yan kasuwar suna tafiya ne a cikin babur mai uku wanda aka fi sani da Keke NAPEP, inda ‘yan bindigar sun bude musu wuta a kusa da wurin, inda suka kashe mutum daya nan take, wasu kuma suka jikkata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP. William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, onda ya ce an kai hari kan ‘yan kasuwar, wasu sun jikkata kuma an daukesu zuwa asibitin Abejukolo, hedikwatar karamar hukumar Omala.
Ya ci gaba da cewa, Kwamishinan ‘yan sanda, CP Edward Egbuka, ya hada rundunar ‘yan sanda da jami’an sa-kai zuwa wurin da lamarin ya faru domin zakulo wadanda suka aikata laifin da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.
A halin da ake ciki, babban basaraken karamar hukumar Omala, HRH Boniface Musa, Ojogba na Ife, ya yi Allah wadai da wannan danyen aikin.
Ya yi tir da hare-haren da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai wa al’ummar Bagana, inda ya koka da yadda kisan ya lalata shirin zaman lafiyar da Atta Igala da HRM Alaji Mathew Opaluwa Akpa da sauran masu ruwa da tsaki suka shirya.
A WANI LABARIN KUMA: Yanzu-Yanzu: Wani Tsohon Dan Majalissar Wakilai Ya Rasu
Wani Tsohon dan majalisar wakilai mai suna Tayo Sarumi ya rasu.
DAILY POST ruwaito cewa, ta samu labarin cewa Sarumi ya rasu da yammacin jiya Juma’a.