
Yan bindiga sun hallaka wani marubuci Dan jam’iyyar APC a Ondo
Yan ta’adda wadanda ake kyautata zaton ‘yan fashi ne sun hallaka marubuci Dan jam’iyyar APC na Jahar Ondo mai suna Dele Isibor.
KARANTA:-Manyan Motoci biyar da kanana biyu sun kama da wuta a Ogere
Dele ya mutu ne a ranar litinin bayan gajeruwar jinya da yayi da aukuwar lamarin.
Alex Kalejaye mai magana da yawun Jam’iyyar APC na Jahar yace Dele ya kasance jajurtace ne wajan ya tabbatar da cigaban jam’iyyar a Jahar.