Hukumar kula da Ilimin Yara ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ta bayyana cewa a shekarar nan da muke ciki wato 2021, masu garkuwa da mutane sun kai hari a Makarantun Nijeriya har sau 20, inda suka yi awon gaba da Dalibai 1,436.
A cewarsu wannan matsalar ta ‘yan fashin Dajin ta hana yara kimanin Miliyan Daya komawa Makarantunsu.
Inda suka bayyana hakan a matsayin koma bayan ilimi a yankin da lamarun ke faruwa.