Wasu ‘yan bindiga da suka kai farmaki a garin Idon da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna sun yi garkuwa da akalla mutane 22 a ranar Laraba.
Wata majiya ta ce mutane hudu ne suka jikkata a harin da aka kai da sanyin safiyar ranar.
“Ba mu san yadda suka zo ba amma kawai mun ji suna harbi, suna karya kofa da tagogi. Sun zo ne da misalin karfe 12:30 na safe,” in ji shi.
Jami’an jihar da na ‘yan sanda har yanzu ba su tabbatar da faruwar harin ba amma kansilan mai kula da harkokin mulki da kudi da lafiya na karamar hukumar Bala Jonathan ya bayyana wadanda harin ya rutsa da su.
Ya ce, “A yayin harin, an sace mutanen kamar haka: Justina Joseph, Mary Joseph, Rejoice Joseph, Stephen Joseph Samson Ladan, Christiana David, Boniface David, Helen Aminu, Mirabel Aminu, Precious Philemon, Nelson Philemon da Christian Philemon.
“Sauran su ne Yosi Gabriel, Stephen Clement, Jinkai Musa, Derrick Obadiah, Daniel David, Paul David, Istifanus Peter, Miracle Matthew, Jesse Charles da Favor Daniel.”
Jonathan ya bayyana sunayen wadanda suka jikkata: David Maigaya, Micah Musa, Josephine Matthew da Marshall Musa.