Yan bindiga sun Kai Hari a wasu Kauyuka dake Jihar Neja
A daren jiya Juma’a ne Yan bindigan suka afka kauyukan Kuchi, Kurrubako da Guni cikin Karamar Hukumar Munya.
Yan bindigan sun hallaka mutane biyu lokacin da suka shiga Kauyukan.
KARANTA:- Bayan dogon lokacin da aka iba Kungiyar NDLEA sun sanar da Karin girma wa ma’aikatan 3,506
Duk da cewa Yan sakai dake yankin sunyi kokarin tunkarar Yan bindigan inda suma suka hallaka Yan bindigan guda biyar tare da jikkata wasu da dama.
Jaridar thisday ta ruwaito cewar “Yan bindigan dauke da bindugu kirar AK47 da harsashai sun shiga Kauyukan a Mashina.
Shigansu Kauyan keda wuya suka fara harbin kan me uwa da wabi don firgitan mutanen Kauyen da nufin kore shanu.
An gayama Jaridar thisday ” an kashe Yan bindigan biyar ne sabida tun karar da matasan Kauyukan sukaima Yan bindigan.
Rahotanni dake zuwa an ce Yan bindigan sun tafi da gawawwakin da aka kashe musu.
Alhaji Ibrahim Ahmad Inga darakta na NSEMA yace “yaji labarin aukuwar lamarin amma haryanzu dai babu cikakken bayani dayazo musu a hukumance”.
A WANI LABARIN:- Jaridar PUNCH ta ruwaito Kungiyar kwallon kafa ta Mexico zasu buga wanni biyu a gida ba tare da Yan kallo ba, hukuncin da kungiyar kwallon kafa ta duniya ta yanke.
Kungiyar kwallon kafa ta duniya tace” Youde Shugaban kungiyar yake fada munji irin ihun da magoya bayan kwallon kungiyar Mexico keyi lokacin da ake wasan samun gurbin gasar cin kofin CONCACAF.
Wasan an bugashi ne a filin Akron an Jalisco dake Guadalajara dake kudanci Mexico.
Hukuncin ya hada da cin tarar kungiyar kwallon kudin America 65,000.
Yace ” yazama wajibj magoya bayan kungiyar Mexico dasu daina irin wannan ihun
Yace wannan bashi karo na farko da kungiyar kwallon kafa ta duniya ke cin kungiyar kwallon kafa ta Mexico tara ba. To wannan ya zamo na karshe.