Daga Sulaiman Musa
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan cocin Haske Baptist Church da ke kauyen Manini Tasha a karamar hukumar Chukun ta jihar Kaduna inda suka kashe mutum guda.
Sannan kuma, ‘yan bindigan sun sace masu ibada da dama a yayin wannan harin da suka kai da misalin karfe goma na safiyar yau din nan yayin da kiristoci ke ibada.
Wanda aka kashen an gano sunansa Dakta Zakariah Dogo Yaro, wani likita ne da ke aiki a karkashin ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna.
Jihar Kaduna dai na daga cikin jihohin arewacin Nijeriya da ke fama da matsalar masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga dadi.